Za mu kawo ƙarshen hukunce-hukuncen kotuna masu karo da juna – Ministan Shari’a

0
26
Za mu kawo ƙarshen hukunce-hukuncen kotuna masu karo da juna – Ministan Shari'a

Za mu kawo ƙarshen hukunce-hukuncen kotuna masu karo da juna – Ministan Shari’a

Ministan shari’a kuma babban lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen yadda kotunan ke yin hukunce-hukunce masu karo da juna.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Talata a Ilori wajen buɗe taron kwana uku na kawo sauye-sauye a harkokin shari’a a Najeriya.

Ma’aikatar shari’a ta ƙasa tare da taimakon Ƙungiyar Tarayyar Turai ne ta shirya taron.

Mista Fagbemi, ya ce sabon alkalin alkalan Najeriya a shirye yake ya bayar da haɗin kai wajen yin wannan gyara.

Kuma ya ce shugabancin ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya, ya nuna cewa lallai akwai buƙatar kawo ƙarshen matsalar.

KU KUMA KARANTA: Kama Mabarata a Najeriya: Wani babban lauya ya maka ministan Abuja a kotu

Fagbemi, ya ce sauye-sauyen da ake matuƙar buƙata a ɓangaren shari’a suna da muhimmanci sosai ga tsari da shirye-shiryen gwamnatin yanzu na bunƙasa Najeriya.

Leave a Reply