Za mu kare masu zanga-zanga in dai ta lumana ce – IGP

0
67
Za mu kare masu zanga-zanga in dai ta lumana ce - IGP

Za mu kare masu zanga-zanga in dai ta lumana ce – IGP

Babban sufeton ‘yansadan Najeriya, IGP, ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar zanga-zangar da wasu ‘yan ƙasar ke shiryawa a wata mai zuwa, yana mai cewa “za mu kare masu zanga-zanga matuƙar dai ta lumana ce”.

Sai dai da yake magana bayan ganawa da manyan jami’an rundunar, Kayode Egbetokun ya yi ƙira ga matasa da su haƙura da zanga-zangar “saboda gwamnati na bakin ƙoƙarinta”.

“Idan zanga-zangar ta lumana ce za ku ganmu muna kare masu zanga-zangar.

Ba mu adawa da zanga-zangar lumana, za mu taimaka wa masu zanga-zangar lumana saboda ‘yancinsu ne” in ji shi lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

“Amma kuma akwai alhaki a kanmu na kare rayuka da dukiyoyi.

Ba za mu zauna muna kallon ‘yandaba suna ƙona gine-gine da sunan zanga-zanga ba, ba za mu yarda da wannan ba.”

Ya ƙara da cewa sun samu bayanan yadda wasu ke jiran matasa su kwaikwayi irin zanga-zangar da mutanen Kenya suka yi “kwabo da kwabo” a Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya roƙi ‘yan Najeriya da su dakatar da shirin zanga-zanga

“Ina amfani da wannan damar na yi ƙira ga matasan Najeriya, don Allah ku yi watsi da ƙiran duk wanda ke neman ku fito ku tayar da hankali. Tuni Najeriya ta ɗanɗana matsalolin mummunar zanga-zanga.”

Matasa na cigaba da tattaunawa game da zanga-zangar da masu shirya ta suka ce za a yi daga ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa, musamman a shafukan sada zumunta.

Shi ma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya nemi masu shirya zanga-zangar “su dakata tukunna har sai sun ji irin martanin zai mayar game da koke-kokensu”.

Leave a Reply