Za mu kai Bazoum kotu saboda cin amanar ƙasa – Sojojin Nijar

Daga Ibraheem El-Tafseer

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sun tattara gamsassun hujjoji da shaidar da za a iya gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed a gaban kotu, bisa laifin cin amanar ƙasa.

Sun kuma tuhume shi da yi wa tsaron cikin gida da na wajen ƙasar, zagon ƙasa.

Kakakin sojin Kanal Amadou Abdramane ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ta tashar talbijin ta ƙasar.

Ana sa rai, ƙungiyar raya ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS za ta gudanar da wani taro ranar Litinin ɗin nan don ci gaba da matsa lamba ga sojojin juyin mulki su hau teburin tattaunawa, haka ita ma Majalisar Tsaro da Tabbatar da Zaman Lafiya ta Tarayyar Afirka za ta yi taron don tattaunawa a kan rikicin.

Sojojin na tsare da Bazoum da iyalansa a wani ɗaki na ƙarƙashin ƙasa a fadar gwamnati da ke birnin Yamai, tun bayan hamɓarar da shi a ranar Lahadi 26 ga watan Yulin bana.

KU KUMA KARANTA: Amurka za ta ɗora alhakin kare lafiyar Bazoum a hannun sojojin Nijar

Baya ga shugaban sojojin sun kuma kama wasu daga cikin jiga-jigan gwamnatinsa da ma na jam’iyyarsa ta PNDS Tarayya.

Mai magana da yawun gwamnatin sojin ya ce tuni sun riga ma sun tattara duk wasu bayanai da shaidun da suke buƙata domin gurfanar da Bazoum a gaban shari’a.

A sanarwar, kakakin ya ce, za su gurfanar da Bazoum tare da waɗanda ya ƙira masu haɗa baki da shi a cikin ƙasar da ma ƙetare a kan laifukan da suka zayyana, saboda musayar bayanan da ya yi tsakaninsa da wasu ‘yan ƙasashen waje da shugabannin ƙasashe da kuma shugabannin ƙungiyoyin ƙasashen duniya.

Bayan karɓe mulki tare da rushe zaɓaɓɓiyar gwamnatin tuni suka naɗa majalisar ministoci, tare da yin biris da duk wani ƙira na neman sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya, daga ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO da sauran ƙasashe da hukumomi masu rajin kare dimokraɗiyya na duniya.

Wannan ya janyo suka ɗaga ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma da Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya.

Biris da halin ko-in-kula tare da ƙara kankane iko da kuma riƙe hamɓararren shugaban da sojin ke yi, ya sa ECOWAS ɗaukar matakai daban-daban a kan lamarin ciki har da sanya rundunar sojojinta ta ko-ta-kwana cikin shiri domin ɗaukar matakin soji a yunƙurin mayar da gwamnatin dimokraɗiyyar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *