Za mu inganta tsaro ta hanyar haɗa kan jami’an tsaro da tattara bayanan sirri

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Tinubu ya faɗi haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar ƙasar na ranar murnar cikar ƙasar shekara 63 da samun ‘yancin kai.

Ya ce za su kare rayukan ‘yan ƙasar ne ta hanyar tabbatar da jami’an tsaro sun yi aiki tare da kuma tattara bayanan sirri.

Shugaban na Najeriya ya kuma ce an ɗora wa hafsoshin tsaro nauyin ƙarfafa wa jami’ansu gwiwa wajen aiki tare.

“Ina jinjina tare da yaba wa jami’an tsaronmu kan yadda suke ba mu tsaro. Da yawa sun sadaukar da rayukansu don kare ƙasarmu. Muna tunawa da su a yau da kuma iyalansu.

Tinubu ya ce za a wadata sojoji da kayan aikin da ake buƙata domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *