No menu items!

Sample Page Title

Date:

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christoper Musa ya ce rundunar tsaro za ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a harin da jirgin soji a ƙauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna.

Janar Musa ya sanar a ranar Juma’a cewa da zarar rundunar ta kammala bincike kan harin, duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

Ya shaida wa manema labarai a Hedikwatar tsaro da ke Abuja cewa babu yadda za a zura ido wani ya yi irin wannan aika-aika ba tare da an hukuna shi ba.

KU KUMA KARANTA: Sanatoci sun sallama albashinsu na Disamba ga nutanen Tudun Biri

A cewarsa, “a aikin soja ba ma kare masu laifi, saboda haka za mu yi komai a fili, babu rufa-rufa.

“Mun sha hukunta dakarunmu da ke rundunar Operation Hadin Kai, wasunsu kuma soji ta yanke musu hukuncin dauri a kurkuku.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...