Za mu gurfanar da wasu daga cikin ‘yan kasuwar Singa a kotu – Muhyi Magaji

0
104
Zamu gurfanar da wasu daga cikin 'yan kasuwar Singa a kotu - Muhyi Magaji

Za mu gurfanar da wasu daga cikin ‘yan kasuwar Singa a kotu – Muhyi Magaji

Daga Shafaatu Dauda, Kano

Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado, ya ce zasu gurfanar da wasu daga cikin ‘yan kasuwar Singa a kotu kan zargin yiwa mutane ƙarin fashin kayayyakin masarufi bayan kammala zanga-zangar lumana.

Muhyi, ya bayyana hakane ta cikin shirin barka da hantsi na gidan radiyon Freedom, ya ce hukumar zata gurfanar da wasu daga cikin ‘yan kasuwar Singa ne sakamakon zargin su da yiwa mutane Karin farashin kaya ba bisa doka.

Haka zalika hannu guda kuma ya ce ana gudanar da bincike kan zargin karkatar da aƙalar shinkafar tallafi da gwamnatin tarayya ta baiwa al’ummar Jihar Kano.

KU KUMA KARANTA: An sace biliyan 50 daga asusun gwamnatin Kano – Muhyi Magaji

Ya kuma ce yanzu haka tuni hukumar ta samo oda daga kotu don fara ɗaukar mataki na farko gabanin zuwa gaban alkalin kai tsaye.

Muhyi, ya kuma ƙara da cewa, hukumar za taci gaba da sanya ido don ganin an tabbatar da aiwatar da dai-daiton da aka samar kan ƙarin farashin kayayyakin masarufin.

Leave a Reply