Za mu gudanar da zaɓen Senegal nan ba da jimawa ba – Macky Sall

Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya ce zai gudanar da zaɓen ƙasar “nan ba da jimawa ba” bayan kotun tsarin mulki ta ce matakin da ya ɗauka na ɗage zaɓen ya saɓa wa doka.

Shugaba Sall ya bayyana haka ne ranar Juma’a kwana guda bayan kotun, wacce ita ce mafi ƙarfi kan harkokin zaɓe a ƙasar, ta soke matakinsa na ɗage zaɓen shugaban ƙasar daga ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa watan Disamba mai zuwa.

Matakin nasa ya haddasa ruɗani a ƙasar sannan yana shan suka daga ciki da wajen ƙasar.

Dubban ƴan ƙasar ne suka gudanar da zanga-zangar adawa da ɗage zaɓen a matakin da ƴan hamayya suka bayyana a matsayin juyin mulki.

Mutum aƙalla uku ne suka mutu sakamakon zanga-zangar.

“Shugaban ƙasa zai aiwatar da cikakken hukuncin Kotun Tsarin Mulki,” in ji wata sanarwa da fadarsa ta fitar.

KU KUMA KARANTA: Kotun tsarin mulkin Senegal ta yi watsi da ɗage zaɓen shugaban ƙasa

“Don haka, ba tare da ɓata lokaci ba, shugaban ƙasa zai tuntuɓi waɗanda suka kamata da zummar shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa nan ba da jimawa ba.”

Sall, wanda ya hau mulki a 2012 bayan ya lashe zaɓe, ya ɗage zaɓen da ya kamata a gudanar ne sakamakon abn da ya kira taƙaddamar da ake yi game da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da kuma fargabar sake samun tashin hankalin da aka yi a shekarar 2021 da 2023.

Daga bisani ƴan majalisar dokokin ƙasar sun amince da ƙudurin dokar da ya ɗage zaɓen zuwa ranar 15 ga watan Disamba, bayan jami’an tsaro sun hana ƴan majalisa na jam’iyyun hamayya halartar zaman majalisar.

Wa’adin mulkin Shugaba Sall zai ƙare a watan Afrilu don haka masu sharhi ke gani ya zama wajibi a zaɓi wanda zai maye gurbinsa kafin ya sauka.

Ƴan hamayya sun yi zargin cewa Sall ya ɗage zaɓen ne domin jam’iyyarsa, wadda ta tsayar da Firaiminista Amadou Ba a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa, tana tsoron shan kaye.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *