Za mu goyi bayan ɗan takarar Arewa a matsayin shugaban ƙasa a 2027 – ACF

0
21
Za mu goyi bayan ɗan takarar Arewa a matsayin shugaban ƙasa a 2027 - ACF

Za mu goyi bayan ɗan takarar Arewa a matsayin shugaban ƙasa a 2027 – ACF

Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), ta ce za ta mara wa ɗan takarar shugaban kasa daga Arewa a zaɓen 2027.

Kungiyar ta ce wannan mataki na da nufin ceto yankin Arewa daga gazawar shugabanci da matsalolin da ake fuskanta.

Da yake jawabi a taron Majalisar Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ACF da aka gudanar a Kaduna, Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Mamman Mike Osuman, ya bayyana ƙalubalen da ke fuskantar yankin.

Ya ce akwai rashin tsaro, talauci, da rashin adalci.

Ya yi ƙira ga ‘yan Arewa su haɗa kai don inganta yankin tare da duba ayyukan shugabanni.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ACF ta buƙaci sojoji su gaggauta murƙushe sabuwar ƙungiyar ta;addanci, Lakurawa

Osuman ya yi tambaya ko shugabannin Arewa suna ɗaukar matakan da suka dace don magance matsalolin cikin gida, kamar haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, rashin tsaro, da ƙarancin wayar da kai.

Ya kuma yi ƙira ga haɗin gwiwa tsakanin shugabanni, sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki don shawo kan waɗannan matsalolin.

Ƙungiyar ACF ta nuna goyon bayanta ga ƙungiyar League of Northern Democrats (LND), wata sabuwar ƙungiya da ta dukufa wajen magance matsalolin yankin Arewa, ciki har da rashin aikin yi, ilimi, da tasirin siyasa.

Osuman ya jaddada buƙatar haɗin kai da shirye-shiryen da za su taimaka wajen kyautata makomar Arewa.

Leave a Reply