Daga Ibraheem El-Tafseer
Ƙungiyar raya tattalin arziƙin Ƙasashen Afirka na Yamma (ECOWAS) ta ce ba za ta gaji ba, za ta ci gaba da amfani da hanyar diflomasiyya wajen ganin ta janyo hankalin ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso na ganin ba su aiwatar fa aniyarsu ba ta ficewa daga cikinta.
Ecowas ta cimma hakan ne a ƙarshen tattaunawar da ministocin harkokin wajen mambobinta suka gudanar a yau a Abuja, domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a yankin.
KU KUMA KARANTA: ECOWAS ta buƙaci hukumomin Senegal su sanya ranar gudanar da zaɓe
Ecowas ta faɗa cikin ruɗani tun bayan da ƙasashen Nijar da Burkina da Mali suka sanar da aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar.
Ana tsaka da haka sai ga wani rikici na neman ɓulluwo a Senegal da ke ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar.
Cikin dokokin Ecowas na fita daga ƙungiyar, sai mambanta ya sanar da ita shekara guda gabanin ficewar, wani abu da ƙasashen suka sa kafa suka yi fatali da shi.
Sanadiyyar hakan ne ƙungiyar ta ce ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ba su bi hanyoyin da suka dace na fita daga ƙungiyar ba.