Za mu biya diyyar harin Mauludin Kaduna – Ministan Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin biyan diyyar masu taron Mauludin da harin bom daga jirgin soja ya kashe a Jihar Kaduna.

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ne ya sanar da haka, sa’o’i kaɗan bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin.

Ministan ya bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro da Gwamnatin Kaduna za su yi aiki tare wajen gudanar da bincike kan abin da ya faru a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Harin dai ya auku ne a lokacin da wata makatar Islamiyya take gudanar da bikin Mauludi a ranar Lahadi da dare a ƙauyen Tudun Biri, wanda ya samu halartar baki daga ƙauyukan da ke kusa da su.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta tabbatar mutum 85 sojoji suka kashe bisa kuskure a Kaduna

Ana tsaka da taron ne wani jirgi mara matuƙi mallakin Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ya yi mahalarta taron ruwan bama-bamai.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 85 a harin baya ga wasu 66 da suka samu raunuka.

Wani magidanci, Malam Musa, ya ce ƙanana 12 a gidansu harin ya kashe, ciki har da ’ya’yansa shida, maza uku da mata uku, da kuma ’ya’yan ’yan uwansa guda shida.

Sarkin Garin Tudun Biri, Malam Suleiman Shu’aibu ya ce al’ummar garin sun saba gudanar da tarukan Mauludi ba tare da wata matsala ba, sai a wannan karon.

A nasa ɓangaren, Sarkin ƙauyen Ifira, ɗaya daga cikin ƙauyukan da harin ya ritsa da mutanensu a wurin taron, Malam Balarabe Garba, ya yi ƙira ga gwamnati ta biya diyyar waɗanda harin jirign sojin ya shafa.

Al’ummar sun buƙaci gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya faru, da nufin hana aukuwar irin haka a nan gaba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *