Za mu ƙara haɓaka alaƙarmu da sabon zaɓaɓɓen shugaban Amurka – Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayyar ta bayyana shirinta na yin haɗin gwiwa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, yayin da yake shirin karɓar ragamar mulki a matsayin shugaban Amurka na 47.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da aka ɗage, Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya jaddada cewa Najeriya na mutunta muradun ɗaukacin ƙasashe.
KU KUMA KARANTA: Shugabannin Afrika na ci gaba da aika wa Trump saƙon taya murna
Ministan ya kuma nanata ƙudirin shugaban ƙasa Bola Tinubu na tabbatar da dimokraɗiyya.