Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), Antonio Guterres, ya rubuta wasiƙa ga kwamitin tsaro na majalisar, inda ya nemi ’yan kwamitin su taimaka don kauce wa mummunar annoba a Gaza.
“Yayin da ake fuskantar shiga bala’in rasa agaji a Gaza, ina neman Kwamatin ya taimaka wajen kauce wa aukuwar bala’i, kuma ya nemi a tsagaita wuta don kai agaji,” in ji Guterres a cikin wani saƙo da ya walafa ranar Laraba.
Cikin wasiƙar da ya rubuta, Guterres ya nanata cewa yanayin na ƙara ƙazancewa cikin sauri, ta yadda ba za a iya gyara wa Falasɗinawa komai ba daga baya da kuma tsaron yankin.
Ya ƙara jaddada buƙatar tsagaita wuta saboda yadda lamarin ke ƙara ƙazancewa a Gaza, da kuma neman zaman lafiya a yankin.
Guterres yace “wannan ne karon farko da nake ɗaukar irin wannan mataki tun bayan zama na sakatare janar na MƊD a 2017”.
KU KUMA KARANTA: Ghana na karɓar baƙuncin taron MƊD kan aikin sojojin wanzar da zaman lafiya
Bugu da ƙari, Guterres ya ce alhakin ƙasashen duniya ne su shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin.
Ya yi amfani da ayar doka ta 99 ta MƊD, wadda ta ba shi damar jawo hankalin Kwamatin Tsaro kan “duk wani batu da yake ganin zai iya barazana ga zaman lafiyar duniya da tsaro”.
Guterres wanda ke ƙira da a “tsagaita wuta cikin gaggawa” tun daga ranar 18 ga Oktoba – ya kuma bayyana “mummunan wahalar ɗan Adam, lalacewar jiki da kuma raunin gaba ɗaya a duk faɗin Isra’ila da yankunan Falasɗinawa da ta mamaye.”
A yayin da ake ci gaba da kai hare-haren, Mista Guterres ya ce ya yi imanin lamarin “na iya ƙara tsananta barazanar da ake fuskanta na wanzar da zaman lafiya da tsaron ƙasa da ƙasa.”
Ya yi gargaɗin cewa zaman lafiyar jama’a a Gaza na iya wargaje wanan ba da jimawa ba a daidai lokacin da tsarin ayyukan jin kai ke durƙushewa.
“Halin da ake ciki yana ƙara taɓarɓarewa zuwa wani bala’i wanda zai iya haifar da tasiri ga Falasɗinawa gaba ɗaya da kuma zaman lafiya da tsaro a yankin.”
“Ina tsammanin zaman lafiyar jama’a zai wargaje nan ba da jimawa ba saboda hali mai tsanani da ake ciki, wanda hakan zai sa ko da taimakon jin kai ba zai yiwu ba,” in ji shi.
Haka kuma, ya yi nuni da cewa, sama da mutane 1,200 a Isra’ila ’yan Hamas sun kashe suka a ranar 7 ga Oktoba, ciki har da yara 33, da kuma mutane 130 da har yanzu ake tsare da su.
“Dole ne a sake su ba tare da wani sharaɗi ba. Batun cin zarafin jima’i a lokacin waɗannan hare-haren yana da ban tsoro,” in ji shi.
Ya jaddada cewa idan aka tsagaita wuta, akwai fatan zaman lafiya da kuma damar kai agajin taimako.
Amma duk da haka, jakadan Isra’ila na Majalisar Ɗinkin Duniya, Gilad Erdan bai amince da ƙiran da Mista Guterres ya yi kan mataki na ayar doka ta 99 ta MƊD ba.