Za a samu sauƙi a farashin mai kwanan nan – IPMAN

0
419
Za a samu sauƙi a farashin mai kwanan nan - IPMAN

Za a samu sauƙi a farashin mai kwanan nan – IPMAN

A yayin da ake raɗe-raɗin cewa farfaɗo da aikin matatar man Warri ya kawo ragi a farashin litar mai kasa da sa’o’i 48 da labarin farfadowar matatar, alkaluma daga gidajen mai a sassan birnin Abuja daban-daban sun nuna cewa an sami ragi a farashin litar mai ne cikin kwanaki 3 zuwa 5 da suka gabata.

Alƙaluma da muka tattaro daga gidajen mai kamar su Total, Azman, Conoil, AYM Shafa sun nuna cewa farashin litar mai a birnin tarayya Abuja na tashi ne daga naira dubu 1 da 20 zuwa dubu 1 da 93, farashin da ya sha bamban da na gidajen man Salbas, sai kuma NNPC da suke sayarwa a kan naira 965 daga kwanaki uku da suka gabata ya zuwa yau kamar yadda zaku ji bayani.

Tun bayan da labarin farfaɗo da aikin tace ɗanyen mai a matatar man Warri ya karaɗe kafafen yaɗa labarai ne masu ruwa da tsaki daga sassan Najeriya daban-daban, ciki da shugaba Bola Tinubu, gwamnoni, masana da wasu ‘yan kasa, ke marhaban da wannan ci gaban, duk da cewa akwai wasu mutane da basu gamsu da gaskiyar aikin ko dorewar shi ba duk da yake sun ga faifan bidiyon da ya nuna hakan.

A wani ɓangare kuma, babban jami’a a ƙungiyar dillalan man fetur na Najeriya, Alh. Zarma Mustapha, ya bayyana cewa tashin matatun man fetur na Fatakwal da Warri ba karamin aikin bunkasa samun wadatar mai zai yi ba a daidai wannan lokaci kuma an fara ganin fa’idar hakan a kasa sakamakon gogayyar cinikayya tsakanin matatu wanda ya yi sanadin ragin da aka gani a farashin litar mai daga watan Nuwamba zuwa yau.

Dangane da batun ko akwai yiyuwar fara samun tatacen mai daga matatar Warri, Alh. Zarma Mustapha ya ce ba’a fara fitar da man fetur ba, sai dizal da kalanzir wanda gidajen man NNPC kawai zasu rika samu a halin yanzu.

KU KUMA KARANTA: Matatar mai ta Warri ta fara aiki – NNPCL

Saidai shugaban kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPCL, Mallam Mele Kyari, ya jadada irin aikin da matatar na Warri ke yi a halin yanzu wanda ke fita da man Dizal, Kalanzir da Nafta.

Dangane da yiyuwar fara aikin saura matatun man fetur na Najeriya da suka daina aiki a baya kamar na Kaduna da sabon matatar Fatakwal, Mallam Mele Kyari ya ce ayyuka sun yi nisa a wadannan matatun kuma nan bada jimawa ba zasu ba wa al’ummar kasa mamaki don zasu fara aiki gadan-gadan.

Najeriya dai na da manyan matatun mai guda huɗu waɗanda suka haɗa da na Warri wacce ta daina aiki a shekarar 2015, sabuwar matatar Fatakwal, tsohon matatar man Fatakwal saii ta Kaduna wadanda a shekarun baya duk sun daina aiki.

Idan Ana iya tunawa, a ƙarshen watan Nuwamba ne matatar man Fatawkal ta koma aiki.

A baya dai, kamfanin NNPCL ya danganta rufe matatun man ƙasar guda 4 da ƙalubalen da ake fuskanta wajen isar da danyen mai zuwa wadannan matatun saboda yadda masu fasa bututu mai suka lalata su lamarin da ya kai ga samun gazawa a yawan danyen mai da ake iya tace wa.

Leave a Reply