Za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohi 19 a faɗin Najeriya – Gwamnatin tarayya
Daga Jameel Lawan Yakasai
Gwamnatin tarayya ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai yawa na tsawon kwanaki biyar, wanda kan iya haddasa ambaliya a jihohi 19 da wurare 76.
Sashin kula da ambaliya na Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, ce ya fitar da wannan gargaɗi a jiya Talata, inda ya bukaci al’umma da masu ruwa da tsaki da su ɗauki matakan kariya cikin gaggawa.
KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ta rushe gidaje da dama a garin Zakirai da ke Kano
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ambaliya mai muni ta afkawa jihohin Ogun da Gombe a ranar Talata, yayin da wasu jihohi kamar Legas, Filato, Anambra, da Delta su ma abin ya shafe su.
A cewar hasashen ambaliya da cibiyar ta bayar, za a iya samun ruwan sama mai ƙarfi wanda zai haifar da ambaliya daga 5 ga watan Agusta zuwa 9 ga Agusta, 2025, a waɗannan yankuna.









