Za a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin Najeriya – Nimet

0
111

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan kare lafiya ba, to akwai yiyuwar mazauna Abuja, Kano, da sauran jihohin Arewa da dama za su fuskanci tsananin zafi wanda zai shafi lafiyarsu.

Tsananin zafi dai na janyo cutuka da dama waɗanda za su iya kai wa mutuwa, kuma hakan a faruwa ne a lokacin da jiki ya kasa sarrafa zafin.

Mazauna waɗannan jihohin na iya fuskantar matsanancin zafi, wanda zai sa su shiga yanayi mara kyau, a cewar Nimet.

“Mun sake shiga lokacin zafi. Ya kamata jama’a su ɗauki matakan da suka dace,” kamar yadda “NiMET ta yi gargaɗi.

KU KUMA KARANTA: Jihohin Kogi, Anambara da Yobe za su fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a daminar bana – NiMet

Ta ce Abuja, Kano, Sokoto, da Kogi ne za su fi fuskantar tsananin zafi, inda ta shawarci mazauna yankunan da su ɗauki matakin kariya da ya kamata.

Wasu jihohin da ke cikin rukunin fuskantar zafin sun haɗa da Kebbi, Katsina, Adamawa, Gombe, Bauchi, Taraba, Neja, Zamfara, Nasarawa, Jigawa, Benue, da kuma Kwara.

NiMET ta kuma gargaɗi mazauna jihohin Osun, Ekiti, Ondo, Bayelsa, Akwa Ibom, Anambra, Delta, Enugu, Edo, Ogun, Plateau, Borno, Imo, Abia, da Cross River da cewa su kasance cikin shiri don karuwar zafi, duk da cewa zafin ba zai yi tsanani ba kamar na sauran jihohi.

Shawarwarin Nimet na yadda za a gujewa tsananin zafi

A rika shan ruwa a-kai-a-kai
A rika zama a wuraren da ke da sanyi domin hutawa
Kada a bar yara a cikin mota a rufe idan ba ta tafiya
Ka saka bakin gilashi da malafa idan za ka fita waje
Ka saka kaya marasa nauyi kuma masu shara-shara
Kada ka shiga rana, sannan kada a fita waje tsakanin karfe 12 na rana zuwa 4 na yamma.

Leave a Reply