Za a fuskanci ɓarkewar kwalara, rashin abinci da tsaro a Maiduguri – MƊD

0
95
Za a fuskanci ɓarkewar kwalara, rashin abinci da tsaro a Maiduguri – MƊD

Za a fuskanci ɓarkewar kwalara, rashin abinci da tsaro a Maiduguri – MƊD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi game da yiyuwar ɓarkewar cutar kwalara a sansanonin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da aka kafa a Maiduguri, babban birnin Borno sakamakon ambaliyar ruwa da ya mamaye jihar.

Rahoton da ofishin kula da ayyukan bada agaji na Majalisar Dinkin Duniyar ya fitar, yace abubawan da za’a bukata cikin gaggawa sun hada da abinci da tsaro da wurin kwana da kuma tsaftataccen ruwa, inda ya kara da cewar wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurbace, kuma na iya janyo barkewar cututtuka irinsu kwalara.

An ruwaito rahoton na cewa, “buƙatun gaggawa da ake dasu sun hada da abinci da matsuguni da tsaftataccen ruwan sha, saboda wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurbace.

Tsaro na daga cikin muhimman abubuwan damuwa, musamman ga yaran da basa tare da kowa ko suka rabu da danginsu da tsofaffi da masu bukata ta musamman.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa a Maiduguri ta shafe wasu sassan garin (Bidiyo)

Wuraren da ambaliyar tafi shafa a birnin Maiduguri sun hada da Gwange da Hanyar Bama da Gidan Namun Daji da Gidan Waya da Sakatariyar Jihar da Titin Legas da Fadar Shehun Borno da babbar kasuwar Maiduguri da yankunan Custom da Gamboru da Budum da Asibitin Kwararru da kuma gaba dayan yankin gidan waya.

Mutane da dama sun rasa matsugunansu, sai dai mahukunta, sun shaida cewa wasu sun soma komawa gidajensu.

Leave a Reply