Za a fara dandaƙe masu yin fyaɗe a Kaduna

0
177

Gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada shirinta na gudanar da aikin tiyatar cire marena ga mazajen da suka yi fyaɗe da kuma tiyatar salpingectomy ga takwarorinsu mata.

Ku tuna cewa a shekarar 2022, tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya sanya hannu kan dokar da aka yi wa gyaran fuska ta 2020 wacce ta tanadi yin tiyatar cire marena ga maza da cire bututun fallopian ga mata masu yiwa yara fyaɗe bayan an same su da laifi.

A watan Nuwamba 2020, majalisar dokokin Kaduna ta amince da yanke hukunci a matsayin hukunci ga duk wanda aka samu da laifin fyade a jihar.

Kwamishiniyar aiyuka da ci gaban jama’a, Madam Rabi Salisu, ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki na jinsi da aka gudanar a Kaduna a ranar Alhamis 30 ga watan Nuwamba, 2023.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Kebbi ta ɗaure yaron da ya yi wa ƙananan yara biyu fyaɗe

Ma’aikatarta ce ta shirya taron ƙolin, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Haɗin Kai da Shirye-shiryen Lafiya (CIHP).

Salisu ta ce matakin na ladabtarwa na ƙunshe ne a cikin dokar hana cin zarafin jama’a da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa (VAPPL), ta shekarar 2018.

Leave a Reply