Zaɓen 2027: Zan bar wa duk wani matashin da ke son takarar shugaban ƙasa a ADC – Atiku

0
189
Zaɓen 2027: Zan bar wa duk wani matashin da ke son takarar shugaban ƙasa a ADC - Atiku
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar

Zaɓen 2027: Zan bar wa duk wani matashin da ke son takarar shugaban ƙasa a ADC – Atiku

Daga Jameel Lawan Yakasai

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai janye daga takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027 idan wani ɗan takara matashi ya doke shi ya lashe tikitin jam’iyyar ADC.

Atiku ya ce zai goyi bayan irin wannan ɗan takara tare da zame masa jagora.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba zai iya tabbatar da ko zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa ba.

“Wannan shi ne farkon tafiya. Abin da muke bai wa muhimmanci shi ne gina jam’iyya da kuma samun magoya baya masu ƙarfi,” in ji Abubakar lokacin da aka tambaye shi ko zai tsaya takara.

“Iidan na tsaya takara, kuma wani matashi ya doke ni, zan amince da hakan. Jam’iyyar da muka shiga yanzu tana bai wa matasa da mata muhimmanci.”

Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a 2023, da kuma tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, duka sun nuna sha’awar samun tikitin ADC.

KU KUMA KARANTA: Babu alamar Tinubu zai iya magance talauci da yunwa a Najeriya – Atiku 

Abubakar ya fice daga jam’iyyar PlPDP a watan Yuli, inda ya zargi jam’iyyar da kauce wa ginshiƙan da aka kafa ta a kai.

Ya shaida wa BBC Hausa cewa ya bar PDP ne saboda ‘yan leƙen asiri daga jam’iyyar APC sun shigo ciki.

“Haka ma shi ne ɗaya daga cikin dalilan da suka sa muka kafa ADC, wadda ni ma ɗan jam’iyyar ne,” in ji shi.

Leave a Reply