Zaɓen 2027: Ba mu cimma yarjejeniyar haɗewa da PDP, NNPP ba – Peter Obi
Gabanin zaɓen 2027 da ke tafe, ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce har yanzu ba su kai ga cimma yarjejeniyar haɗewa tsakanin PDP da NNPP dama wata jam’iyya ba.
Tsohon gwamnan jihar Anambran ya bayyana hakan ne da safiyar yau Alhamis yayin ganawarsa da manema labarai akan halin da kasa ke ciki.
KU KUMA KARANTA:Baƙin haure 27 sun mutu a gaɓar tekun Tunisiya
Ya kara da cewar har yanzu ba’a kai ga kulla yarjejeniya da wata jam’iyya ba. Ya bukaci dukkanin masoyan Najeriya a fagen siyasa su dunkule a wuri guda a 2027 domin kayar da jam’iyyar APC, wacce ya zarga da yin wadaka da dukiyar kasa.
Haka kuma, Obi ya yi magana kan yanayin tsaron da Najeriya ke ciki da abin takaici, inda yace ‘yan Najeriya na mutuwa a kullum babu gaira ba dalili saboda ayyukan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Obi ya kara da cewa, har yanzu matsalar cin hanci da rashawa bata ragu ba haka tsadar gudanar da gwamnati abinda sabbaba yawan basussukan da gwamnatin jam’iyyar apc mai ci ta Shugaba Bola Tinubu ke kara yin tashin gwauron zabo