Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Tinubu ya yi ganawar sirri da Betara

0
905

A ranar Talata ne mai neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta 10, Muktar Betara, ya yi wata ganawar sirri da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Betara, memba mai wakiltar mazaɓar Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar ta jihar Borno, ya yi ta nuna goyon bayansa ga takararsa na shugaban ƙasa tare da membobin jam’iyyar, zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wakilai, tsofaffin ‘yan majalisa da sauran masu ruwa da tsaki.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na yaƙin neman zaɓen Betara ya bayar a Abuja ranar Laraba.

KU KUMA KARANTA: Shugaban ƙasa mai jiran gado, Tinubu ya dawo gida, ya ce “a shirye nake da aikin da ke gaba”

“Yaƙin neman zaɓe da tuntuɓar Betara da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na ɗaya daga cikin shawarwarin da ya fara a cikin watanni uku da suka gabata gabanin rantsar da shi a watan Yuni.

“Betara wanda a halin yanzu yake shugabantar kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Wakilai, a baya ya yi musabaha tare da babban kwamandan mai jiran gado jim kaɗan bayan wani zaman daukar hoto.

“Ziyarar tuntuɓar Betara ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ta faru ne a sabon gidansa da ke gidan tsaro da ke Abuja, bayan dawowar shi daga hutu da kuma aikin Hajji mai ƙaramin ƙarfi a Saudiyya,” in ji jami’in yaƙin neman zaɓen.

Leave a Reply