Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano zai sake duba batun tsige Sanusi – Kwankwaso

3
393

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce gwamnati mai zuwa a Kano za ta sake duba batun tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 14.

Sanusi wanda ya zama sarki a wa’adin ƙarshe na Kwankwaso a matsayin gwamna, Gwamna mai barin gado Abdullahi Ganduje ne ya tsige shi, wanda shi ne mataimakin gwamna a lokacin da aka naɗa sarkin.

An cire Sanusi ne a ranar 9 ga Maris, 2020, sannan kuma an kore shi daga Kano aka aika shi zuwa garin Loko, wani yanki mai nisa a jihar Nasarawa, yayin da ake binciken kuɗaɗen masarautar da ke ƙarƙashinsa.

Ganduje ya kuma raba masarautun gida biyar ya naɗa sarakunan da suka yi daidai. Sai dai da yake magana a wani faifai na bidiyo, Kwankwao ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf, zaɓaɓɓen gwamna, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, zai duba batun tsige masarautun.

KU KUMA KARANTA: 2023: Atiku, Kwankwaso, Obi da Tinubu sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

“Mun yi yaƙin neman zaɓe kuma kamar yadda kuka sani muna da farin jini a Najeriya musamman a jihar Kano, yanzu mun dawo kuma in Allah Ya yarda za mu ci gaba da ayyukan alheri da gwamnatinmu ta bari.

Wannan gwamna mai jiran gado da tawagarsa za su ɗauke su.” “A matsayinmu na dattawa, za mu ci gaba da ba su shawarar yin abin da ya dace. Mun yi ƙoƙarin ka da a sa baki a batun kawo ko tsige wani sarki, amma yanzu dama ta zo.

“Waɗanda aka bai wa wannan dama za su zauna su duba batutuwan. Za su duba abin da ake sa ran yi. Bayan Sarki, hatta Masarautar ta rabu gida biyar. Duk waɗannan suna buƙatar yin nazari.

Galibi shugaba yakan gaji alheri, mummuna da al’amuran da suke da wuyar sulhu”. Ya kuma yi addu’ar Allah ya dafa wa Gwamna mai jiran gado damar tafiyar da al’amura cikin sauƙi.

3 COMMENTS

Leave a Reply