Yunƙurin tsagaita wuta a Sudan ya ci tura, ana ta ruwan harsasai

2
349

Tuni dai yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Sudan da ta fara aiki a ranar Alhamis ta lalace, inda aka kai hare-hare ta sama da kuma luguden wuta a kusa da fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin kasar Khartoum da safen Alhamis, a cewar Al-Jazeera.

An kuma ji ƙarar harbe-harbe a garin Omdurman da ke maƙwabtaka da shi, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana a shafin Twitter.

Yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta na mako guda da ɓangarorin biyu a rikicin Sudan suka amince da ita ya kamata ta fara aiki daga ranar Alhamis har zuwa ranar 11 ga watan Mayu.

KU KUMA KARANTA: Ɓangarorin da ke gaba da juna a Sudan sun amince da tsagaita buɗe wuta

Sai dai ana ganin damar da za ta iya kasancewa ta yi kaɗan. Tun lokacin da aka fara faɗa a Sudan tsakanin ɓangarorin soji masu biyayya ga manyan janar-janar biyu kusan makonni uku da suka gabata, an sha yin shawarwarin tsagaita buɗe wuta na tsawon sa’o’i 72, sai dai an sha karyawa.

Shugaban ƙasar Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ne ke jagorantar sojoji a fafatawa da tsohon mataimakinsa, Mohammed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar Rapid Support Forces (RSF).

Janar-janar biyu sun taɓa ƙwace iko da Sudan tare a wani juyin mulkin haɗin gwiwa da sojoji suka yi.

Sai dai kuma rashin jituwar da aka yi ta yi kan yadda za a raba madafun iko ya haifar da ɗa mai ido a tsakanin sansanonin biyu, wanda ya kai ga faɗa a fili a ranar 15 ga Afrilu, ya kuma jefa ƙasar da mazaunanta kusan miliyan 46 cikin wani mummunan rikici.

2 COMMENTS

Leave a Reply