Yukiren ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙi na Rasha sama da 70

0
140

Yukiren ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuki guda 71 da Rasha ta kai mata hari da su a cikin dare, harin da ta bayyana a matsayin mafi girma tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da mamaya a kanta.

Rundunar sojin Yukiren ɗin ta ce akasarin jiragen ƙirar Iran ne, kuma ta kakkaɓo su ne a baban birnin ƙasar, Kyiv, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wutar lantarki, a yayin da yanayin sanyi a ƙasar ya tsananta.

Tun da farko ta ce ta kakkaɓo jirage 71 daga cikin 75 da aka kai mata hari da su, daga baya kuma ta ce ta harbo 74. A wani jawabi da ya  yi ta talabijin, Kakakin sojin saman ya ce 66 daga cikin jiragen da suka kaddamar da harin an kakkaɓo su ne a Kyiv da garuruwan da ke kewayen sa.

KU KUMA KARANTA: Rasha ta harbo jiragen Yukiren marasa matuƙa 31 a yankunan kan iyaka

Harin jirage marasa matukan na zuwa ne a daidai lokacin da Yukiren ke bikin tunawa da ranar Holodomor,  lokacin da miliyoyin mutane suka shiga yanayi na tsananin yunwa a shekarar 1930 ƙarƙashin shugaba Josef Stalin na Tsohuwar Tarayyar Soviet.

Leave a Reply