Yawan waɗanda aka kashe a harin Jihar Filato ya kai 113

0
161

Adadin waɗanda suka mutu a hare-haren da aka kai a ƙarshen mako a jihar Filato ya ƙaru zuwa 113, in ji wani jami’i a ranar Litinin, a yankin da ake yawan samun rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Neptune Hausa ta rawaito cewa, rundunar sojin Najeriya a ranar Lahadi tana cewa mutum 16 ne suka mutu a sabbin hare-haren.

Wannan dai shi ne tashin hankali mafi muni da ya ɓarke a Filato tun watan Mayu, lokacin da aka kashe fiye da mutum 100 a hare-haren manoma da makiyaya.

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Bokkos a Jihar Filato, Monday Kassah, ya ce an kashe mutum 113 a hare-haren da aka kai a ranakun Asabar da Lahadi.

“Hare-haren sun kasance waɗanda aka tsara su sosai. Aƙalla al’ummomi daban-daban 20 ne ‘yan bindiga suka kai wa hari,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: An kashe mutum 16 a wani hari a Jihar Filato

“Mun gano gawarwakin mutum 113 daga cikin wadannan al’ummomi, mun kuma gano sama da mutum 300 da suka jikkata.”

Kassah bai bayyana ko su wane ne ke da alhakin kai hare-haren ba. Ya ƙara da cewa an kai waɗanda suka jikkata asibiti.

Jihar Filato dai na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da rikicin bambancin ƙabila da addini, inda irin waɗannan rikice-rikicen suka yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane a ‘yan shekarun nan.

Ana yawan kallon tashin hankalin a matsayin rikicin ƙabilanci da addini tsakanin makiyaya Musulmai da galibin manoman Kiristoci. Amma sauyin yanayi da faɗaɗar aikin noma su ma manyan abubuwa ne da ke taka rawa wajen ta’azzarar rikicin.

Leave a Reply