Yawan Falasɗinawan da aka kashe a hare-haren Isra’ila sun kai 21,500 — Ma’aikatar Lafiya ta Gaza

0
198

Aƙalla Falasɗinawa 187 aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza a cikin awa 24 da suka wuce, adadin da ya sa yawan waɗanda suka mutu zuwa yanzu ya kai 21,507 tun 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma’aikatar Lafiya da ke yankin da aka yi wa ƙawanya.

Ma’aikatar ta kuma ƙara da cewa mutum 55,915 ne suka jikkata tun bayan yaƙin da Isra’ilan ta fara a yankin.

Tun bayan ɓarkewar mummunan yaƙin Isra’ila a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, fiye da kashi 80 cikin 100 na al’ummar Gaza miliyan 2.4 aka raba da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Leave a Reply