Yawan Falasɗinawan da Isra’ila ta kashe a Gaza sun haura dubu bakwai

0
155

Hukumar Lafiya ta Zirin Gaza ta ce yawan Falasɗinawan da suka mutu sanadin hare-haren Isra’ila yanzu sun haura 7,000.

Kazalika, Hukumar Kula da Ayyukan Jinƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA) ta sanar a ranar Alhamis cewa kaso 68 na mutanen da aka kashe mata ne da ƙananan yara.

Hukumar dai ta ce ta samu alƙaluman ne daga ƙungiyar Hamas da ke mulkin Zirin na Gaza.

Kusan mutum 1,600 ne kuma kawo yanzu ake tunanin sun ɓace ɓat a yankin.

KU KUMA KARANTA: An kashe iyalan ɗan jaridan Aljazeera a Gaza

Sai dai har yanzu hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar a yankin na sama ne, inda ta ce tana nan tana shirin ƙaddamar da wani ta ƙasa.

Tun a ranar bakwai ga watan Oktoba ne dai Hamas ta ƙaddamar da hare-haren a kan Isra’ila, kafin ita kuma ta mayar da martani.

Isra’ilar dai ta ce hare-haren na Hamas sun kashe mata mutane sama da 1,400, sannan aka yi garkuwa da sama da 222 ta ƙarfin tsiya.

Sai dai daga bisani an saki huɗu daga cikin Yahudawan da aka kashe.

Leave a Reply