Yawaitar bashin da Najeriya ke karɓowa abin damuwa ne – Tajuddeen Abbas
Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya nuna damuwa kan yadda bashin Najeriya ya ƙaru zuwa Tiriliyan 149.39 a farkon 2025, kwatankwacin dala biliyan 97, wanda ya wuce iyakar kashi 40% da doka ta gindaya, inda ya kai 52% na GDP.
Abbas ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara na ƙungiyar WAAPAC a Abuja, yana mai cewa hauhawar bashin na barazana ga dorewar tattalin arziki, tare da gargadin cewa rancen da ke tallafa wa cin hanci da ciyar da bukatu bai kamata a ci gaba da shi ba.
KU KUMA KARANTA: Majalisar Dattawa ta amince shugaban ƙasa ya aro Naira Tiriliyon 1.77
Ya ce dole rance ya kasance domin ayyukan raya kasa kamar hanya, lafiya, ilimi da masana’antu.
Abbas ya kuma bayyana shirye-shiryen Najeriya na jagorantar kafa tsarin sa ido kan bashin majalisun dokoki a Yammacin Afirka domin tabbatar da gaskiya da tsari.
Kakakin ya jaddada cewa Majalisa za ta tabbatar da amincewar jama’a kafin karɓar manyan rance, tare da sauƙaƙa rahoton bashi ga ‘yan ƙasa, domin inganta gaskiya da dorewar tattalin arziki.








