Yau ce ranar Hausa ta duniya
Daga Ibraheem El-Tafseer
A yau Litinin 26/08/2024 ya yi daidai da ranar da aka ware a matsayin Ranar Hausa ta duniya, inda Hausawa za su tuna da abubuwan da suka ginu akai na al’ada haɗe da addini da sauran su.
Harshen Hausa abin alfahari ne duba da yadda harshen ya samu ɗaukaka a faɗin Duniya. Harshe ne wanda ya ke da kalmomi masu yawan gaske, Hausawa suna da al’adu masu ban sha’awa da ƙayatarwa sosai wanda hakan ya sa duniya take girmama harshen game da al’adunsa.
Ranar Hausa da turanci “Hausa Day” rana ce da aka keɓance ta domin nuna muhimmancin harshen Hausa, tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen ya ke fuskanta.
KU KUMA KARANTA: Gargajiya a ƙasar Hausa
Ana gudanar da bikin Ranar Hausa ne a kowacce ranar 26 ga watan Agusta inda bayan shafukan sada zumunta, akan gudanar da hira a dandali daban-daban da kuma gidajen watsa labarai da gidajen TV don bayyana muhimmanci da harshen ya ke da shi.
A shekarar 2022 an gudanar da wannan biki inda a lokacin Hausawa suka baje kolinsu a shafukan sada zumunta wajen fito da karin magana iri-iri.
Kamar kowacce shekara bana ma ranar ta zagayo inda jama’a za su ci gaba da taya juna murna.
Haƙiƙa, muna matuƙar alfahari da harshen Hausa dama Hausawa.