Yara biliyan 1.4 ne suke rayuwa cikin matsanancin talauci a duniya — MƊD

Yara biliyan ɗaya da miliyan ɗari huɗu ƴan ƙasa da shekaru 16 ne a faɗin duniya suka gaza samun kowanne irin tallafin kariya na zamantakewar al’umma.

Wannan yanayin ya bar yaran cikin mawuyacin hali ta hanyar fuskantar cututtuka da rashin abinci mai gina jiki da kuma talauci, a cewar wani sabon rahoto da hukumomi biyu na Majalisar Ɗinkin Duniya tare da ƙungiyar agaji ta British Charity Save the Chirldren ta fita a ranar Laraba.

Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO) da Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da Save the Children ne suka tattaro bayanan.

A ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi, ƙasa da kashi 10 cikin 100 na yara ne suke samun tallafin da ya kamata yara su samu, yanayin da ke nuna gagarumin bambanci da ke tsakani idan aka kwatanta da damarmakin da yara waɗanda ke ƙasashe masu arziki suke samu.

”A duniya baki ɗaya, akwai yara miliyan 333 da ke rayuwa cikin matsanancin talauci inda suke rayuwa kan kasa da dala 2.15 a kowace rana, sannan kusan yara biliyan daya ne suke fuskantar nau’in talauci iri daban-daban,” a cewar Natalia Winder Rossi, Darakta a sashen da ke kula da tsare-tsare da kuma samar wa al’umma kariya na UNICEF.

KU KUMA KARANTA: Australia ta goyi bayan ƙudurin MƊD na tsagaita wuta a Gaza

“A halin da ake ciki a yanzu, ba a kai ga cimma muradun ci gaba mai ɗorewa kan talauci ba, kuma ba za a amince da hakan ba,” in ji ta.

Rosi ta ce, kawo ƙarshen matsalar talauci tsakanin yara zaɓin tsari ne da gwamnatoci suke ɗauka.

Faɗaɗa ayyukan samar da kariya ga yara a yaƙin da ake yi da talauci yana da matuƙar muhimmaci, gami da samar da ci gaban kowanne yaro a duniya, in ji ta.

Kungiyoyin sun ce tallafa wa yara na da matuƙar muhimmaci wajen samar musu kariyar da ake da niyyar yi don inganta rayuwarsu na tsawon lokaci.

Ana ba da su a matsayin tsabar kuɗi ko kuɗin haraji, sannan tallafin yara yana da muhimmaci wajen rage talauci da kuma ba da damar kula da lafiya da samar da abinci mai gina jiki tare da samar da ingantaccen ilimi da ruwa mai tsafta.

Kazalika tallafin na taimaka wa wajen samar da ci gaban al’umma ta fuskar tattalin arziki, musamman a lokutan rikici.

Yara da dama sun gaza samun abubuwanan da suke buƙata na yau da kullum don kauce wa talauci don haka suke fuskantar barazanar tasirin da yunwa ke haifarwa da rashin samun abinci mai gina jiki da kuma gaza kaiwa wani mataki na rayuwa.

Bayanan sun yi nuni da cewa a tsawon shekaru 14 an samu matsakaicin kari a tallafin da yara suke samu a duniya, daga kashi 20 cikin ɗari a shekarar 2009 zuwa kashi 28.1 a 2023.

Adadin ɗaukar bayanan yaran da ke ƙasashe wadanda ke fama da matsalar sauyin yanayi na ƙasa sosai idan aka kwatanta da ƙasashen da ba a sanya su a matsayin wadanda ke cikin haɗari ba.

Tabbatar da cewa yara sun samu kariyar zamantakewa ta al’umma shi ne mabuɗin kare su daga duk wani tasirin mummunan tashin hankali na sauyin yanayi, a cewar ƙungiyar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *