‘Yansandan Abuja sun kama buhuhunan wiwi da dillalan ƙwaya 11

0
311
'Yansandan Abuja sun kama buhuhunan wiwi da dillalan ƙwaya 11
Tarin wiwi da 'yansanda suka kama a Abuja

‘Yansandan Abuja sun kama buhuhunan wiwi da dillalan ƙwaya 11

Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen birnin Abuja ta ce ta kama mutum 11 da zargin safarar miyagun ƙwayoyi a wasu samame da ta kai a wasu lokunan birnin.

Wata sanarwa a shafukan sada zumunta ta ce samamen sun kai ga gano buhun tabar wiwi 68.

KU KUMA KARANTA: NDLEA a Kano ta kama tabar wiwi da kwalaben Akurkura dubu 8

“Kamen wani ɓangare ne na yunƙurin daƙile ayyukan safara na gungun ‘yanƙwaya da kuma rage aikata laifukan da shan ƙwaya ke haifarwa a birnin,” in ji SP Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar a Abuja.

Leave a Reply