No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yansanda sun kama mutane 4 da ake zargi da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci

Jami’an rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina sun kama wani da suke zargi da daukar nauyin ayyukan ta’addanci, Aminu Hassan, a bisa zarginsa da agazawa ‘yan bindigar da suka addabi ƙaramar hukumar Danmusa da kewayenta.

Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a sanarwar daya fitar a jiya Talata.

Yace wanda ake zargin mai shekaru 25 ya fito ne daga kauyen Dundubus na karamar hukumar Danja ta jihar.

Ya ci gaba da cewa kamen wani ɓangare ne na nasarar da rundunar ta samu a yakin da take yi da ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Abuja sun kama sojoji na jabu tare da motoci 296 na sata

An kama wanda ake zargin ne yayin sintirin yau da kullum akan babbar hanyar ‘Yan Tumaki zuwa Kankara a ranar 19 ga watan Nuwamban daya gabata a ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar.

An ce mutumin na ɗauke da khakin soja guda 2 da aka ɓoye a cikin bakar jakar leda.

A yayin gudanar da bincike, an kama ƙarin waɗanda ake zargi da hannun a lamarin da suka hada da (1) Lawal M. Ahmad, mai shekaru 29 dana (2) Isma’il Dalhatu, mai shekaru 24, dukkaninsu daga Unguwar Basawa, ta ƙaramar hukumar Sabon-Garin Zariya a jihar Kaduna da (3) Shafi’u Adamu, mai shekaru 28, daga ƙauyen Danjaba, a ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...