‘Yansanda sun kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

0
6
'Yansanda sun kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

‘Yansanda sun kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

’Yan Sanda a Ƙasar Zambiya, sun kama wasu bokaye biyu da ake zargin an bai wa aikin yi wa shugaban ƙasar, Hakainde Hichilema, asiri.

A cewar rundunar ’yan sandan ƙasar, an kama Jasten Mabulesse Candunde da Leonard Phiri a Lusaka, babban birnin ƙasar.

Sun ce aikin da aka bai wa bokayen shi ne amfani da tsafi domin cutar da shugaban ƙasar.

A kudancin Afirka, mutane da dama sun yi imani da bokaye, inda tsoron asiri ke sa mutane rayuwa cikin fargaba a wasu lokuta.

’Yan sanda sun bayyana cewa Nelson Banda, wanda ƙani ne ga wani ɗan majalisa mai suna Emmanuel Banda, da aka fi sani da “Jay Jay” Banda, ne ya bai wa bokayen don wannan aikin.
A cewar rahoton, Nelson ya tsere bayan an kama bokayen.

Rundunar ta ce za su ci gaba da farautar sa har sai an kama shi.

KU KUMA KARANTA: An ja hankalin yan Najeriya kan shirin ƙungiyoyin asiri na ɗaukar sabbin mambobi

A watan da ya gabata, an kama ɗan majalisar, Emmanuel Banda, a Zimbabwe kan zargin fashi, wanda ya musanta aikatawa.

’Yan sanda sun ce an kama bokayen ƙarƙashin dokokin tsafi na Zambiya.

An same su da guraye da layu da kuma wata hawainiya mai rai, wanda hakan ya ƙara tabbatar da zargin aikata tsafi.

Sun kuma ce suna zargin bokayen na amfani da dabbobin don yin asiri.

Bokayen sun bayyana cewa an yi musu alƙawarin kuɗi har kimanin kwaca miliyan biyu, kwatankwacin dala 73,000, idan har sun kammala aikin cutar da shugaban ƙasar.

Wannan ya sa ‘yan sanda ke ƙara bincike kan yadda aka tsara wannan aiki na tsafi da kuma sauran waɗanda ake zargi suna da hannu a ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here