‘Yansanda sun cafke tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano

0
64
'Yansanda sun cafke tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano
Muhuyi Magaji Rimin Gado, 'Yansanda sun cafke tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano

‘Yansanda sun cafke tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta nuna damuwa kan kama tsohon shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado, da rundunar ‘yansanda ta yi ba tare da gabatar da takardar kamu ko umarnin kotu ba.

A wata sanarwa da Antoni Janar na Jihar ya fitar, rahotanni sun ce an kama Muhyi a ofishinsa na aikin lauya da ke kan titin Zaria kafin a tafi da shi zuwa Abuja, duk da cewa akwai umarnin kotu da ya hana hakan.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci GTBank ta biya naira miliyan 5 ga Muhuyi Rimingado daga asusun gwamnatin Kano

Gwamnati ta bayyana lamarin a matsayin barazana ga tsarin mulki da hakkin dan Adam, tana zargin cewa wasu ‘yan siyasa na kokarin amfani da hukumomin tsaro don haifar da matsala a jihar.

Sanarwar ta ce ana ganin kamen na da alaka da wasu manyan bincike da shari’o’in cin hanci da Magaji ke da muhimman bayanai a kansu.

Gwamnatin Kano ta bukaci ‘yansanda su bayyana dalilin kama shi, tare da jaddada bukatar bin doka da kare hakkin jama’a, tana kuma kiran jama’a da su zauna lafiya yayin da ta ci gaba da bibiyar lamarin.

Leave a Reply