‘Yansanda a Yobe sun kama ’yar shekara 54 kan safarar makamai

0
60
'Yansanda a Yobe sun kama ’yar shekara 54 kan safarar makamai

‘Yansanda a Yobe sun kama ’yar shekara 54 kan safarar makamai

’Yansanda sun kama wata mata mai shekeru 54 kan zargin ta da fasakwaurin harsashi guda 350 a Jihar Yobe.

Rundunar ’yansandan jihar na zargin matar ne safarar makamai ba bisa ka’ida ba daga garin Buni Yadi zuwa Damaturu.

Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce dubun matar ta cika ne a Damaturu bayan samun bayanan sirri a kan ayyukanta.

“An kama wata mota ƙirar Golf 3 kuma bayan bincike an gano harsasai guda 350 samfurin 7.62x39mm a ɓoye a cikin kayan wadda ake zargin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga satar makaman jami’an tsaro suka yi – Ministan Tsaro

“A halin yanzu ana yi mata tambayoyi domin gano abokan cin mushenta da kuma manufarsu,” in ji shi.

Dungus ya ruwaito kwamishinan ’yansanda na Jihar Yobe, Garba Ahmed, yana jaddada aniyarsa ta yaki da laifuka tare da ƙira ga jama’a su ci gaba da ba wa jami’an tsaro  haɗin kai.

Leave a Reply