‘Yansanda a Kano sun kama wani ƙasurgumin ɗan daban da ake nema ruwa a jallo
Daga Shafaatu Dauda, Kano
Rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta samu nasarar cafke matashin nan mai suna Inuwa Zakari, wanda akafi sani da Gundura, bisa zargin da ake yi masa da addabar al’ummar Ɗorayi da faɗace-faɗacen daba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a birnin Kano.
Sanarwar ta ce an kama Gundura ne a ranar 26 ga watan Oktoban 2024, a lokacin da ya dawo jihar don tayar da fitina, a zaben kananan hukumomin da aka gudanar.
Wannan nasarar ta zo ne bayan sumamen da rundunar ta yi daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Oktoba 2024 tare da kama wasu mutane 14 da ake zargi da aikata laifuka maban-banta.
KU KUMA KARANTA: Yansanda a Yobe sun kama ’yar shekara 54 kan safarar makamai
Haka zalika ana zargin gundura da haɗa kai da wasu mutane wajen kaiwa kwamandan bijilanti farmaki har suka sare masa hannu da kuma barnata motar yan sanda a wurare daban-daban.
Yanzu haka dai waɗanda ake zargin suna babban sashin gudanar da binciken manyan laifukan na CID , inda rundunar ta tabbatar da cewa da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.