’Yansanda a Kano sun kama mutum 3 da jabun kuɗi

0
18
’Yansanda a Kano sun kama mutum 3 da jabun kuɗi

’Yansanda a Kano sun kama mutum 3 da jabun kuɗi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum uku da aka samu da jabun kuɗi har Naira biliyan 129.

Kakakin rundunar, SP Haruna Kiyawa ne, ya bayyana wa manema labarai a Kano ranar Talata cewa jabun kuɗin sun haɗa da Dalar Amurka, CFA da Naira.

Ya ce adadin kuɗin da aka ƙwato sun haɗa da dala 3,366,000, CFA51,970,000, da Naira 1,443,000.

SP Kiyawa, ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin, suna hannun ‘yan sanda kuma suna taimakawa wajen bincike don gano inda ake buga jabun kuɗin.

KU KUMA KARANTA: An kama malaman bogi a jami’ar Bayero da ke Kano

Baya ga kuɗin, ’yan sanda sun kuma ƙwato harsasai guda shida, Adaidaita Sahu guda uku, babura guda takwas da kuma jakunkuna uku ɗauke da tabar wiwi.

Sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da ƙwayoyi 250 na diazepam, tumaki 278, da shanu guda bakwai.

Kiyawa, ya ce kama waɗannan mutane na nuna yadda rundunar ke ƙoƙarin yaƙi da laifuka a Kano.

Ya ƙara da cewa rundunar ta magance manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, da kuma rikicin daba.

Leave a Reply