‘Yansanda a Kano sun kama mutane 2 kan zargin zuba ruwan rubutu a Rijiya

0
32
'Yansanda a Kano sun kama mutane 2 kan zargin zuba ruwan rubutu a Rijiya

‘Yansanda a Kano sun kama mutane 2 kan zargin zuba ruwan rubutu a Rijiya

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da zuba ruwan rubutu, a cikin wata Rijiya dake ƙauyen Durmawa, a ƙaramar hukumar Bebeji ta jahar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce tun a ranar 9 ga watan Disamba 2024, suka samu ƙiran daga garin Durmawa, da cewar an kama wasu mutane biyu sun zuba wani abu, a cikin rijiyar dake garin.

Bayan samun rahotanne kwamishinan yan sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya tura dakarun yan sanda zuwa wurin, inda aka taho da mutanen guda biyu, inda daya daga cikinsu mai suna, Ado Ahmad, ɗan shekaru 35 mazaunin unguwar Tudun Murtala a birnin Kano, ya tabbatar da cewa ” Tabbas shi ne ya zuba rubutu a cikin Rijiyar”.

KU KUMA KARANTA: Yansanda sun kama mutane 4 da ake zargi da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci

SP Kiyawa, ya ƙara da cewa lokacin da aka kamo waɗanda ake zargin an samu sauran rubutun a leda kulli goma 15 da kuma wani ƙullin magani guda 5.

”Ya tabbatar da cewa shi yana kasuwancin magani kuma shi ne ya yi wannan rubutu, sannan yaje wannan rijiya, ya zuba wani ɓangare na rubutun don ya samu kasuwa”

A nasa ɓangaren wanda ake zargin Ado Ahmad, ya ce shi mai bayar da magani ne, na hawan jini, Ciwon Hanta da kuma bawa matan da basa haihuwa, kuma ya zuba rubutun ne don ƙara bunƙasa kasuwancinsa.

A ƙarshe SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yanzu haka wanda ake zargin yana hannun yan sanda ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Leave a Reply