‘Yansanda a Borno sun kama 1 daga cikin fursunonin da suka tsere

0
72
'Yansanda a Borno sun kama ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere

‘Yansanda a Borno sun kama 1 daga cikin fursunonin da suka tsere

Rundunar ’yansandan Jihar Borno, ta yi nasarar sake cafke ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere a birnin Maiduguri na Jihar Borno, biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku.

Fursunan mai suna, Abubakar Mohammed, mai shekara 27, wanda ya tsere daga gidan yari a Maiduguri, biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku.

A ranar 15 ga watan Satumba, 2024, da misalin ƙarfe 3 na rana, wani mazaunin unguwar Bulakara da ke ƙaramar hukumar Gubio, ya sanar wa ‘yan sanda rahoto game da ganin fursunan.

Majiyar ’yan sanda ta ruwaito cewar, jin wannan rahoto ke da wuya ta tawaga ta musamman wadda ta samun nasarar cafke shi.

Rundunar ta ce za ta miƙa Abubakar ga hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Fursunoni 281 sun tsere a Maiduguri sakamakon ambaliyar ruwa – NCS

Har wa yau, ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin zaƙulo ragowar da suka tsere.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron jama’a.

Kazalika, ta yi kira ga jama’a da su bayar da bayanai kan duk wani abu da suke zargi a a yankunansu domin tallafa wa ƙoƙarin ‘yan sanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here