Yankunan da ake tafka yaƙi a Sudan sun ƙara yawa

0
263

Wuraren da dakarun sojan Sudan da na rundunar Rapid Support Forces (RSF) ke fafatawa sun ƙaru a garuruwan Yammacin Kordofan, da Khartoum, da kuma Darfur.

Shaidu sun faɗa wa BBC Arabic cewa an ƙara jibge dakarun sojan Sudan a birnin Al-Fula na jihar ta Kordofan, suna masu cewa ƙazamar fafatawar da ɓangarorin suka yi ta lalata sassan birnin da yawa.

A Nyala, babban birnin jihar Darfur ta Kudu, shaidun sun ce faɗa ya ɗan lafa, amma ana ci gaba da jin ƙarar harbe-harbe.

KU KUMA KARANTA: Ana ta ƙara gwabza faɗa a Sudan ‘yan sa’o’i kaɗan kafin yarjejeniyar tsagaita wuta

Mazauna yankin sun ce arangamar da aka shafe kwana uku ana yi ta ɗaiɗaita yankin, yayin da ake ci gaba da kashe fararen hula.

A gefe guda kuma, jami’an sojan Sudan sun tabbatar da cewa sun yi ruwan wuta kan wasu sansanonin RSF a kudancin birnin Khartoum.

Wata majiya ta ce hare-haren sun fi ƙamari a unguwannin Jabra, da Abu Adam, da kuma Kalakia.

Leave a Reply