Yankunan Bwari, Kuje da Abaji suka fi haɗarin rayuwa a Abuja – FCTA

0
211

Lura da yadda matsalar tsaro ke neman zama ruwan dare a sassan Najeriya, hukumomin Abuja sun bayyana yankunan Bwari da Kuje da kuma Abaji a matsayin mafiya haɗari wajen rayuwar jama’a saboda yawaitar satar mutane ana garkuwa da su.

Ma’aikatar dake kula da Abujan tace duk wasu manya manyan garkuwa da mutanen da aka gani a Abuja sun fito ne daga waɗannan yankuna, duk da yake akan samu wasu a wasu yankuna na daban.

Daraktar kula da mulki da kuma kuɗaɗe na ma’aikatar babban birnin tarayyar, Ebele Molokwu ce ta sanar da haka lokacin da take ganawa da manema labarai domin karin bayani akan ayyukan da sashen ta ya gudanar a wannan shekara.

KU KUMA KARANTA: An yi garkuwa da wasu matan aure 8 a gona a Abuja

Molokwu tace yankin Abuja ya yi iyaka da wasu jihohi da matsalar tayi ƙamari, wanda hakan kan bai wa masu aikata wannan laifi damar kutsa kai Abuja suna satar mutane lokaci zuwa lokaci.

Jami’ar tace suna ɗaukar matakai wajen amfani da dabarun zamani domin tinkarar matsalar wajen ganin sun daƙile ta, saboda muhimmancin birnin Abuja da kewaye, da kuma yawan mutanen dake zama a ciki.

Leave a Reply