’Yan ƙwadago za su fara yajin aiki saboda kama shugabansu

0
165

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya na NLC da TUC sun ayyana tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba don nuna bacin ransu da harin da aka kai wa shugabansu na ƙasa, Joe Ajaero, a Jihar Imo.

Aminiya ta rawaito yadda aka zargi jami’an ’yan sandan da suke aiki tare da Gwamnan Jihar da lakada wa Joe duka yayin wata zanga-zangar ’yan kwadago a Jihar, a makon da ya gabata.

Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja ranar Juma’a, Babban Sakataren TUC na ƙasa, Nuhu Toro, wanda ya sami rakiyar wasu shugabannin NLC, ya kuma ce sun buƙaci a gaggauta canza wa Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ahmed Barde, wajen aiki daga Jihar.

KU KUMA KARANTA: Ba kama shugaban ‘yan ƙwadago muka yi ba — ’Yan sanda

Ya ce, “’Yan sanda sun kumbura wa Kwamared Joe Ajaero idanu, sun masa dukan tsiya, sun tozarta shi, sun yaga masa rigar mutunci, sannan sun kai shi wajen da ba a sani ba, suka ci gaba da azabtar da shi, har aka yi masa barazanar kisa.

“Sai dai daga bisani ya sami ɗauki daga wajen mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

“Sai dai saboda tsananin dukan da ya sha, sai da ’yan sanda suka kai shi asbitinsu. Amma a lokacin da muka ziyarce shi a can, idonsa ya kumbura, ya yi ja, ba ma ya iya gane mutane.

“Duk jikinsa ya kukkumbura. Ba ma ya iya tafiya sai an taimaka masa. A sakamakon haka, tilas muka ɗauke shi muka kai Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Owerri don a ci gaba da duba lafiyarsa.

“… Saboda haka, muddin gwamnati ta gaza cika kowanne daga cikin sharuɗan da muka fi gaya mata, NLC, TUC da rassansu ba za su ci gaba da aiki ba a ƙasar nan daga ranar Laraba mai zuwa, 8 ga watan Nuwamban 2023.

“Kazalika, ƙungiyoyin biyu za su gudanar da taron Gamayyar Majalisun Zartarwarsu, domin ɗaukar mataki na gaba,” in ji Nuhu Toro.

Leave a Reply