’Yan ƙungiyar IPOB sun hallaka wasu sojojin Najeriya
Wasu da ake kyautata zaton mayaƙan ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) ne sun hallaka wasu sojojin Najeriya da ke aiki a yankin Kudu maso Gabas.
Mahara sama da 15 ne ɗauke muggan makamai suka kai hari kan sojojin da ke sintiri a mahaɗar Obikabia da ke Aba a Jihar Abia a ranar Alhamis.
Rahotanni daga yankin sun ce bayan ’yan IPOB ɗin sun harbe sojojin ne suka sa wa motar sintirin wuta.
Mai magana da yawun haramtacciyar ƙungiyar, Emma Powerful, ya ayyana 30 ga Mayu a matsayin ranar juyayin tunawa da mayaƙan Biafra.
Ya kuma umarci ’yan yankin Kudu maso Gabas su zauna a gida dole, domin jinjina ga mayaƙan Biafra da sojojin Najeriya suka hallaka a yakin basasa.
A wannan rana, ’yan ta’addar sun tilasta an rufe gidajen mai, da bankuna, da manyan gidajen cin abinci, da manyan kantuna a fadin kudu maso kudancin Najeriya.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun gano wurin da IPOB ke haɗa jirage marasa matuƙa
Jama’ar jihohi biyar da ke yankin sun yi biyayyar dole ne saboda fargabar ta’addancin ’yan ƙungiyar ta IPOB.
Da yake mayar da martani game da harin, Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Benjamin Kalu, ya ce “Waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki ba su da wani dalili.
“Rashin gaskiya ce kawai tsagwaronta, da zalunci, da rashin imani da kuma rashin la’akari da halin rayuwa.”
Kalu ya jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ya kuma bai wa da hukumomin sojan Najeriya tabbacin daukar matakan da suka dace don taimakawa wajen bankado waɗanda suka kitsa harin domin hana sake samun irin haka a nan gaba.