‘Yan yawon buɗe ido da dama ne suka maƙale sakamakon ambaliya a Kenya

0
130

Kimanin ‘yan yawon buɗe ido ɗari ne suka makale a wani kogin da ya cika sakamakon ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya a sanannen wurin ajiyar Maasai Mara na kasa a kudu maso yammacin Kenya.

Canjin yanyi da iftila’in El Ninone suka haddasa mummunar ambaliya a kasar da ke gabashin Afirka, wanda ya kai ga lalata hanyoyi, gadoji da sauran ababen more rayuwa.

Aƙalla mutane 179 ne suka mutu tun cikin watan Maris a bala’o’in da suka shafi ambaliyar ruwa, a cewar gwamnati.

“Akwai kusan ‘yan yawon buɗe ido ɗari” da ke maƙale a cikin gidaje da sansanonin da dama.

Daya daga cikin jami’an gundumar Narok ta Yama , Stephen Nakola, ya shaida wa kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP cewa “Wannan adadi ne na farko saboda yawancin sansanonin ba sa isa.

KU KUMA KARANTA: Mutane 7 sun ɓace bayan hatsarin jiragen helikwaftan sojin Japan

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce ta ceto mutane fiye da 90 da suka makale a sansanonin, wasu daga cikinsu ta jirgin sama.

 “A wasu sansanonin, an kwashe tantuna” yayin da wata gada ta lalace, in ji kungiyar.

Wurin ajiyar Maasai Mara, ya kasance wani wurin shakatawa ne, da ake samun namun daji da suka hada da zakuna, giwaye, karkanda, damisa, raƙumin dawa, da wasu sauren su, wadanda ke jan hankalin masu yawon buɗe ido daga ko’ina cikin duniya.

Yawon shakatawa na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen waje na ƙasar Kenya.

Kuɗaɗen shiga masu alaƙa da yawon buɗe ido sun yi tsalle da kashi 31.5% a cikin 2023 idan aka kwatanta da 2022.

Ministan yawon buɗe ido Alfred Mutua ya ce “sansanoni da dama ne lamarin ya shafa” ya kuma buƙaci dukkan gidajen kwana ko otal da sansanonin da ke kusa da koguna da wuraren shakatawa na kasa da su kasance cikin shirin ko ta kwana a batun da ya shafi kwashe mutane”.

Shugaban ƙasar William Ruto ya sanar a jiya Talata cewa ya tattara sojoji tare da ba da umarnin kwashe mutanen da ke zaune a yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliya a kasar.

Tun daga watan Maris, mutane 179, ciki har da yara 15, suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa. Wasu mutane 90 ne suka ɓace yayin da wasu fiye da 195,000 suka rasa matsugunansu.

Leave a Reply