‘Yan uwan Bazoum ba su ji ɗuriyarsa ba tun 18 ga watan Oktoba

0
175

‘Yan uwan hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum ranar Alhamis sun ce ba su ji labarin halin da yake ciki ba tun ranar 18 ga watan Oktoba, suna masu Allah wadai da yadda ake “kamawa da kuma gudanar da bincike” a kan wasunsu.

Sojoji na riƙe da Bazoum da matarsa da kuma ɗansa a gidansa da ke fadar shugaban ƙasa tun da suka kifar da gwamnatinsa ranar 26 ga watan Yuli.

Sojojin sun ƙi sakarsa duk da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya da ƙungiyoyi da dama suke ta yi.

“Tun ranar 18 ga watan Oktoba, ba mu ji labarin halin da Shugaba Bazoum da matarsa Khadija Mabrouk da ɗansa Salem suke ciki ba a fadar shugaban ƙasa inda ake tsare da su,” kamar yadda ‘yan’uwansa suka bayyana a wata sanarwa da suka fitar.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijar sun soke dokar da ta haramta tafiya ci-rani Turai

“Hukumomin soji sun kama wasu daga cikin danginmu da dama suna kuma bincike a kansu ta salon cusgunawa,” in ji sanarwar.

Lauyan zuri’ar, Ould Salem Said, ya shaida wa manema labarai cewa “mun lura da wani abu da ke faruwa a kan iyalan Shugaba Bazoum.”

A ranar talata ne aka bincike gidajen ɗaya daga cikin ƴayan ƴan’uwan Bazoum da na wani ɗan’uwan nasa a Yamai babban birnin ƙasar, a cewar Said.

Lauyan ya ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da wani kawun Bazoum a ranar lahadin da ta gabata, inda ya ƙara da cewa ya gabatar da koke ga ofishin mai shigar da ƙara na gwamnati kan “sacewa da ƙwace da kuma tsare shi ba bisa ƙa’ida ba”.

Said ya kuma ce an kama ɗan’uwan matar Bazoum a kudancin ƙasar, kuma “an miƙa shi a hannun ‘yan sanda”.

Tun a ranar 26 ga watan Yuli ne shugabannin sojojin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani ke mulkin Nijar.

Leave a Reply