‘Yan ta’adda suna ta cire shukokin mutane a Katsina (Bidiyo)

0
149
'Yan ta'adda suna ta cire shukokin mutane a Katsina

‘Yan ta’adda suna ta cire shukokin mutane a Katsina (Bidiyo)

‘Yan ta’adda suna ta sare haɗe da cire shukokin mutane a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

A wani faifen bidiyo da ya fito, wanda aka nuno wani manomi yana ta rusa kuka, yana bayyana irin yadda ‘yan ta’adda suka sare musu shukoki bayan shukokin sun fara fita. Yana ta bayyana cewa bayan sun kashe kuɗaɗe, sun yi sassaɓe, sun yi huɗa, sun yi shuka, sun yi noma. Bayan shuka ta fito, sai ga shi ‘yan ta’adda sun zo suna ta sare shukar.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya yabawa Gwamnan Yobe kan bunƙasa harkar noma a jihar

Da wannan ne suke kira ga gwamnatin jihar Katsina ta dubi wannan lamari, don ta kawo musu ɗauki.

Leave a Reply