‘Yan ta’adda sun lalata wutar lantarkin Maiduguri zuwa Damaturu
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya tabbatar da lalata babbar layin wutar lantarki mai rarraba wuta zuwa Damaturu a jihar Yobe da Maiduguri a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a kan titin Gombe – Damaturu-Maiduguri, inda aka lalata ginshikin wutar lantarki mai ƙarfin 372-330kv.
A wata sanarwa da Babban Manajan hulɗa da Jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya fitar a Damaturu, ya bayyana cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun yanke ƙafafu huɗu na ginshikin wutar, wanda hakan ya haifar da faɗowarsa sa.
Sanarwar ta bayyana cewa jiniyoyin TCN suna aiki domin samar da wuta ta wucin gadi zuwa Damaturu ta hanyar layin wutar lantarki mai ƙarfin 33kv daga Potiskum.
KU KUMA KARANTA: Ƙarin kuɗin wutar lantarki a Najeriya, ya bar baya da ƙura
Maiduguri kuma za ta dogara ne da gidan samar da wuta na gaggawa har sai matsalar ta warware. Za a fara gyaran ginshikin da ya rushe nan take.
TCN ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa kan kayan wutar lantarki na ƙasa a kai a kai, kuma ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su zama masu kula don samar da tsaro, tare da bayar da rahoton duk wani abin da ake zargi a wuraren da aka ajiye kayayyakin wutar zuwa ga jami’an tsaro ko ofisoshin TCN.