‘Yan ta’adda sun kashe ‘yan sa kai 6 a yankin Tsafe (Hotuna)

0
108

Daga Idris Umar, Zariya

A rana Laraba 2 ga watan Mayu ne yan sa-kai 6 suka rasa rayukansu a garin Magazu dake yankin Tsafe na jihar Zamfara wajen artabu da ‘yan ta’adda daji na yankin.

Rahotanni na cewa suma ‘yan ta’addan an kashe wasu da dama daga cikin su ciki har da wani ƙasurgumin ɗan ta’addan mai suna Aminu Dogo.

An tabbatar da namijin koƙari da gamayyar jami’an tson sukayi tare da yi masu fatan Allah ya ƙara tsaresu.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sa kai sun yi wa limami yankan rago a Zamfara

Cikin yan sa kai da suka rasa rayukansu sun haɗa:
Zaharaddini kamfa, Ibrahim Ɗan baba, Ashiru Mai Rafta, Abdurrashid Haruna, Habibu Tunau, sai Auwal Magazu.

Har yanzu jama’a na cikin firgici a wannan yankin.

Leave a Reply