‘Yan ta’adda a Taraba, sun tashi ƙauyuka 15, sun yi garkuwa da mutane 40

Satar mutanen ya faru ne tsakanin ranakun Litinin, 4 ga watan Agusta zuwa Laraba 6 ga watan Agusta, 2023 lokacin da ‘yan bindigan suka mamaye ƙauyuka da dama a jihar.

Wasu ‘yan ta’adda da ake yi wa laƙabi da ‘yan bindiga, sun yi garkuwa da mutane aƙalla 40 a cikin kwanaki uku a ƙauyuka goma sha biyar na ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraba.

Satar mutanen ya faru ne tsakanin ranakun Litinin, 4 ga watan Agusta zuwa Laraba 6 ga watan Agusta, 2023 lokacin da ‘yan bindigan suka mamaye ƙauyuka.

A cewar rahoton jaridar Daily Trust, wasu da dama da suka haɗa da mata da yara har yanzu ba a gansu ba daga sabbin hare-haren da aka kai a daren Laraba a yankin Garba Chede da ke ƙaramar hukumar Bali.

An bayyana cewa ɗaruruwan mutanen ƙauyen sun tsere daga gidajensu suna ɓoye a cikin daji yayin da, da yawa daga cikinsu suka gudu zuwa garin Garba_Chede.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda, gungun ‘yan Boko Haram sun miƙa wuya

Ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen Garbatau da aka kai wa harin, Musa Mainoma, ya ce mazauna ƙauyukan da lamarin ya shafa sun ƙauracewa yankin kuma yanzu haka suna samun mafaka a garuruwan Garba Chede, Sunkani da Pamamga.

Ya ce da yawa daga cikin waɗanda suka gudu ba a gansu ba, kuma iyaye na ci gaba da neman ‘ya’yansu da suka ɓace.

Mainoma ya bayyana cewa ‘yan bindigar da yawansu ya kai sun hau kan babura kuma sun kai farmaki kan al’ummomin manoma.

Ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutanen ƙauyen da dama tare da yin awon gaba da shanu tare da kwashe kayan shaguna a duk ƙauyukan da suka kai hari.

Wani mazaunin Garba Chede, Dodo wanda ya zanta da jaridar ya bayyana cewa sama da mutane dubu uku da suka tsere daga yankunan manoma a lokacin hare-haren suna samun mafaka a garin Garba Chede.

Ya ce mazauna garin Garba Chede sun bayar da masauƙi kyauta ga waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa.

Umar Babangida, shugaban mafarautan ya shaida wa Aminiya cewa da sanyin safiyar Alhamis ne mafarauta suka shiga yankin da lamarin ya shafa domin fatattakar masu laifin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *