‘Yan ta’adda a Neja sun tare a gidajen al’ummomin da suka tsere

0
186
Yan ta'adda a Neja sun tare a gidajen al'ummomin da suka tsere

‘Yan ta’adda a Neja sun tare a gidajen al’ummomin da suka tsere

Watanni 5 bayan da mazauna garin Allawa da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja su ka arce daga gidajensu sakamakon janye sojoji da aka yi daga garin, rahotanni sun ce ‘yan bindiga da ƴan ta’adda sun tare a cikin gidajensu, har ma sun fara noma gonakinsu.

Ɗaya daga cikin waɗanda su ka tsere daga Allawa ya shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ cewa a sun tura wasu mutane gida don tantance ko za su iya komawa don ci gaba da noma, amma sai suka gamu da ‘yan ta’adda a cikin gidajensu, kuma har sun nome gonakin nasu.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kuma yi amfani da takin da suka sayo kafin su arce daga garin, kana suka banka wa wasu daga cikin gidajen wuta.

A watan Afrilun wannan shekarar ne rahotanni suka karaɗe kafafen yaɗa labaran Najeriya a game da tserewar al’ummar Allawa daga garin nasu, sakamakon janye sojojin da ke ba su tsaro da aka yi daga yankin.

KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yansanda ta nuna damuwa kan ƙaruwar laifukan kisan kai a Kano

A wannan lokacin, mahukuntan jihar Neja sun tabbatar da janye sojojin, amma sun ce ba su da wani iko a kan hakan, su na mai cewa lamari ne da ya shafi rundunar sojin ƙasar, waɗanda suka ce su na janyewa ne don sake ɗamara da dabara.

A halin da ake ciki, mazauna wannan gari na Allawa sun yi ƙira ga gwamnatin jihar data tarayya da zu ɗauke ƙwararan matakan kawar da waɗannan ƴan ta’adda daga garin nasu, domin su samu ssu koma gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here