Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano (CP), Muhammed Usaini Gumel, ya ce hukumar za ta shirya wasan ƙwallon ƙafa tsakanin ƙungiyar ta da wasu ‘yan daban da suka tuba, a wani mataki na tabbatar da gaskiyar tubansu.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wasu mutane 108 da aka kama da laifuka daban-daban a lokacin bikin Sallah da ya gabata.
Ya ce, “Za mu ɓullo da wata hanya ta daban don tabbatar da cewa waɗannan ‘yan daban suna canza rayuwarsu tare da zama mutanen kirki. Har ma za mu shirya gasar wasanni da su. Za mu buga wasan ƙwallon ƙafa.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kashe wani ɗan fashi a babbar hanyar a Gombe
“Yanzu za mu mayar da hankalin mu da idanunmu kan ayyukan ‘yan daba (daba) da ke kunno kai, musamman a cikin babban birnin Kano”, in ji Kwamishinan.
CP Muhammed ya ƙara da cewa sun tsara dabarun aiki da kuma ingantaciyar hanyar tara bayanan sirri domin magance duk wani nau’in laifi da ake aikatawa a ciki da wajen jihar Kano.